5
Ƙaunatacce
Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata;
na tattara mur nawa da kayan yajina.
Na sha zumana da kuma kakinsa
na sha ruwan inabina da kuma madarana.
Ƙawaye
Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye;
ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.
Ƙaunatacciya
Na yi barci amma zuciyata tana a farke.
Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa.
“Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata,
kurciyata, marar laifina.
Kaina ya jiƙe da raɓa,
gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”
Na tuɓe rigata,
sai in sāke sa ta kuma?
Na wanke ƙafafuna,
sai in sāke ɓata su?
Ƙaunataccena ya turo hannunsa ta cikin ramin ƙofar;
zuciyata ta fara juyayi a kansa.
Na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena,
sai hannuna ya jiƙe sharkaf da mur,
yatsotsina suna ɗiga da mur,
a hannuwan ƙofar.
Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa,
amma ƙaunataccena ba ya nan, ya riga ya tafi.
Zuciyata ta damu da tafiyarsa.
Na neme shi amma ban same shi ba.
Na yi ta kiransa amma bai amsa ba.
Masu gadi suka gamu da ni
yayinda suke kai kawo a cikin birni.
Suka yi mini dūka, suka yi mini rauni;
suka ƙwace gyalena
waɗannan masu gadin katanga!
’Yan matan Urushalima, ina roƙonku,
in kun sami ƙaunataccena
me za ku ce masa?
Ku ce masa na suma saboda ƙauna.
Ƙawaye
Mafiya kyau a cikin mata
me ya sa ƙaunataccenki ya fi sauran?
Don me kike roƙonmu mu faɗa masa yadda kike ji?
Ƙaunatacciya
10 Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma,
da ƙyar a sami irinsa ɗaya a cikin dubu goma.
11 Kansa zinariya ce zalla;
gashinsa dogaye ne
baƙi wuluk kamar hankaka.
12 Idanunsa sun yi kamar na kurciyoyin
da suke kusa da ruwan rafi,
da aka wanke da madara
aka kuma kafa kamar kayan ado masu daraja.
13 Kumatunsa kamar lambun kayan yaji
suna ba da turare.
Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana
suna ɗiga da mur.
14 Hannuwansa kamar sandunan zinariyar
da aka sa musu duwatsu masu daraja.
Jikinsa ya yi kamar gogaggen hauren giwan
da aka yi masa ado da duwatsun saffaya.
15 Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar
da aka kafa su a cikin rammukar zinariya.
Kamanninsa ya yi kamar Lebanon,
mafi kyau kamar itacen al’ul nasa.
16 Bakinsa zaƙi ne kansa;
komensa yana da kyau.
Haka ƙaunataccena, abokina, yake
’yan matan Urushalima.