6
Ƙawaye
1 Ina ƙaunataccenki ya tafi,
yake mafiya kyau cikin mata?
Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi,
don mu taimake ki nemansa.
Ƙaunatacciya
2 Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa,
zuwa inda fangulan kayan yaji suke,
don yă yi kiwo a cikin lambun
don kuma yă tattara furen bi-rana.
3 Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne;
yana kiwo a cikin furen bi-rana.
Ƙaunatacce
4 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza,
kyakkyawa kuma kamar Urushalima,
mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
5 Ki kau da idanu daga gare ni;
gama suna rinjayata.
Gashinki yana kama da garken awakin
da suke gangarawa daga Gileyad.
6 Haƙoranki suna kama da garken tumakin
da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka.
Kowanne yana tare da ɗan’uwansa;
babu waninsu da yake shi kaɗai.
7 Kumatunki sun yi kamar rumman
da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
8 Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can,
da ƙwarƙwarai tamanin
da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;
9 amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take,
tilo kuwa ga mahaifiyarta,
’yar lele ga wadda ta haife ta.
’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka;
sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.
Ƙawaye
10 Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir?
Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana,
mai daraja kamar taurari a jere?
Ƙaunatacce
11 Na gangara zuwa cikin itatuwan almon
don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari,
don in ga ko inabi sun yi ’ya’ya
ko rumman suna fid da furanni.
12 Kafin in san wani abu,
sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.
Ƙawaye
13 Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya;
ki dawo, ki dawo, don mu dube ki!
Ƙaunatacce
Don me kuke duban Bashulammiya
sai ka ce rawar Mahanayim?