4
1 Ku iyayengiji, ku ba bayinku abin ke daidai ya kuma dace garesu. Kun sani cewa ku ma, kuna da Ubangiji a sama.
2 Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu'a. Ku zauna a fadake cikin addu'a da godiya.
3 Ku yi addu'a tare domin mu kuma, domin Allah ya bude kofa domin kalmar, a fadi asirin gaskiyar Almasihu. Don wannan ne nake cikin sarka.
4 Ku yi addu'a domin in iya fadinsa daidai, yadda yakamata in fada.
5 Ku yi tafiya da hikima game da wadanda suke a waje, ku yi amfani da lokaci.
6 Bari maganarku ko yaushe ta zama ta alheri. Bari ta zama da dadin ji domin ku san yadda za ku amsa wa kowanne mutum.
7 Game da abubuwan da nake ciki, Tikikus zai sanar maku da su. Shi kaunataccen dan'uwa, amintaccen bawa, shi abokin barantaka na ne a cikin Ubangiji.
8 Na aike shi wurinku don wannan, domin ku iya sanin halin da muke ciki, don kuma ya karfafa zukatanku.
9 Na aike shi tare da Onisimus, amintacce da kuma kaunataccen dan'uwa, wanda daya ne daga cikin ku. Za su gaya maku duk abin da ya faru anan.
10 Aristarkus, abokin sarka na, yana gaishe ku da Markus, dan'uwan Barnaba (wanda a kansa ne kuka sami umarni; in yazo, ku karbe shi),
11 da kuma Yesu wanda ake kira Yustus. Wadannan ne kadai daga cikin masu kaciya abokan aiki na domin mulkin Allah. Sun zama ta'aziya a gare ni.
12 Abafaras na gaishe ku. Shi daya daga cikinku ne kuma bawan Almasihu Yesu ne. Kullum yana maku addu'a da himma, don ku tsaya cikakku da hakikancewa a cikin nufin Allah.
13 Gama ina shaidarsa a kan ya yi aiki da himma domin ku, domin wadanda ke Lawudikiya, da na Hirafolis.
14 Luka kaunataccen likita da Dimas suna gaishe ku.
15 Ku gai da 'yan'uwa dake a Lawudikiya, da Nimfa da ikilisiyar da ke cikin gidanta.
16 Lokacin da aka karanta wannan wasika a tsakanin ku, sai a karanta ta kuma a cikin ikilisiyar Lawudikiya, ku kuma tabbata kun karanta wasika daga Lawudikiya.
17 Ku gaya wa Arkibas, “Mai da hankali ga hidimar da ka karba cikin Ubangiji, don ka cika shi.”
18 Wannan gaisuwa da hannu na ne - Bulus. Ku tuna da sarka na. Alheri ya tabbata a gare ku.