1 Tassalunikawa
1
1 Bulus, Sila, da Timoti zuwa ga Ikilisiyar Tassalonikawa cikin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da Salama su kasance a gare ku.
2 Kullum muna bada godiya ga Allah domin ku dukka, kamar yadda muke ambaton ku a addu'o'in mu.
3 Muna tunawa da ku ba fasawa a gaban Allahn mu da Ubanmu kuma ayyukanku na bangaskiya, da kauna. Da hakurin bege na abinda ke gaba cikin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
4 'Yan'uwa kaunatattu na Allah, Mun san kiran ku,
5 yadda bishararmu ta zo gare ku ba ta magana kadai ba, amma da iko, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, haka kuma tawurin tabbatarwa. Ta haka kuma, kun san irin mutanen da muke acikin ku kuma domin ku.
6 Kun zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji, kamar yadda kuka karbi kalmar cikin tsanani mai yawa da murna tawurin Ruhu Mai Tsaki.
7 Sakamakon haka, kuka zama abin misali ga dukkan wadanda ke Makidoniya da na Akaya wadanda suka bada gaskiya.
8 Gama daga gare kune maganar Allah ta bazu ko ina, ba kuwa Makidoniya da Akaya kadai ba. A maimako, har ma zuwa ko ina bangaskiyarku cikin Allah ta kai. Don haka, bama bukatar muce maku komai.
9 Domin su da kansu suna bada labarin irin zuwan mu gare ku. Suna fadin yadda kuka juyo ga Allah daga bautar gumaka don ku bautawa Allah mai rai.
10 Suna bayyana cewa kuna jiran bayyanar Dansa daga sama, wanda ya tasar daga matattu. Wannan shine Yesu, wanda ya 'yantad da mu daga fushi mai zuwa.