2
1 Domin ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, cewa zuwan mu gareku, ba a banza yake ba.
2 Kun kuma san yadda aka wulakantar damu, aka kuma kunyatar damu a Filibi, kamar yadda kuka sani. Muna nan kuwa da karfin zuciya cikin Allahnmu domin yi maku bisharar Allah cikin fama da yawa.
3 Domin kuwa gargadinmu zuwa a gare ku ba gurbatacciya bace, ko cikin rashin tsarki, ba kuma ta yaudara bace.
4 A maimako, kamar yadda Allah ya amince damu, ya kuma damka mana amanar bishararsa, haka kuma muke yin magana. Muna maganar ba domin mu gamshi mutane ba, amma domin mu gamshi Allah. Domin shi ne yake gwada zuciyarmu.
5 Domin bamu taba yi maku dadin baki ba, ko sau daya, kamar yadda kuka sani, ko kwadayi a asirce, kamar yadda Allah shine shaidar mu.
6 Bamu kuma nemi daukaka daga mutane ko daga gare ku ko kuma wadansu ba. Da mun so da mun mori ikonmu a matsayin manzannin Almasihu.
7 A maimakon haka, mun kaskantar da kanmu a tsakanin ku kamar yadda uwa take ta'azantar da 'ya'yan ta.
8 Don haka muna da kauna domin ku, ba bisharar Allahnmu kadai muke jin dadin yi maku ba, amma harda bada rayukan mu domin ku. Domin kun zama kaunatattu ne a garemu,
9 Kufa tuna, 'yan'uwa, game da aikinmu da famarmu. Dare da rana muna aiki sosai domin kada mu nawaita wa kowane dayan ku. A lokacin da muke yi maku bisharar Allah.
10 Ku shaidu ne, haka ma Allah, yadda muka yi rayuwar tsarki da kuma adalci da rashin abin zargi a wajenku wadanda kuka bada gaskiya.
11 Don haka kun kuma sani yadda muka rika yi da kowannenku, kamar uba da 'ya'yansa, yadda muka yi ma ku garadi da kuma karfafa ku, mun kuma shaida.
12 Domin ku yi tafiya a hanyar da ta dace ga Allah, wanda ya kira ku zuwa ga mulkinsa da kuma daukakarsa.
13 Domin wannan dalili ne yasa muke yi wa Allah godiya a koyaushe. Domin a lokacin da kuka karbi maganar Allah daga wurinmu wadda kuka ji, kun karbeta da gaske ba kamar maganar mutum ba. A maimako, kuka karbeta da gaskiyarta, kamar yadda take, maganar Allah. Wannan kalma kuma ita ce ke aiki a cikin ku wadanda kuka yi bangaskiya.
14 Domin ku 'yan'uwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da ke Yahudiya cikin Almasihu Yesu. Domim kuma kun sha wahala irin tamu daga wurin mutanen kasarku kamar yadda suma suka sha a hannun Yahadawa.
15 Yahudawane suka kashe Ubangiji Yesu da sauran Annabawa, kuma Yahudawane suka koro mu, Basu gamshi Allah ba. A maimako, suna hamayya da dukkan mutane.
16 Sun kuma haramta mana yin magana da Al'ummai domin su sami ceto. Sakamakon haka kuwa kullum suna cika zunubansu. Fushi kuma ya afko kansu daga karshe.
17 Mu kuma, 'yan'uwa, mun rabu daku na karamin lokaci, a zahiri, ba a zuciya ba, mun kuma yi iyakar kokarinmu da marmarin ganin fuskarku.
18 Domin mun yi maramarin zuwa gareku. Ni, Bulus, ba sau daya ba, amma Shaidan ya hanamu.
19 To menene begenmu a gaba, ko murnarmu ko rawanin alfahari, a gaban Ubangijinmu Yesu a ranar zuwansa? Ko ba ku bane, da kuma sauran jama'a?
20 Don kuwa kune daukakarmu da kuma farin cikinmu.