14
Idin Ketarewa da bukin gurasa mara yisti sauran kwana biyu kenan, sai shugabanin firistoci da malaman attaura suka nemi yadda zasu kama Yesu a asirce domin su kashe shi. Suna cewa amma “Ba a lokacin idin ba, domin kada su haddasa hargitsi a tsakanin mutane”. Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana shirin liyafa kenan sai ga wata mace dauke da kwalbar turare mai tamanin kwarai, ta shafa masa a kansa. wasu dake tare da Yesu suka husata, suna kwalbarta da cewa “Ai wannan turare ne mai tsada, ina laifin a sayar a raba wa talakawa kudin? ina dalilin wannan almubazaranci? Sai Yesu yace masu “Ku kyaleta, don me kuke tsauta mata, ai Idan kuna da niyyar taimakon talakawa ko matalauta, suna nan tare da ku ko a yaushe amma ni bazan kasance da ku kullum ba. Macen nan tayi aiki nagari domin shirya jikina ga jana'iza. hakika, Ina gaya maku, duk inda za'a yi bishara a duniya baza a mance da matan nan da hidimar da ta tayi mini ba.” 10 Da jin haka sai Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin manzannin ya ruga zuwa wurin baban firist domin ya bashe shi a garesu, 11 Da mayan firistoci suka ji haka suka yi murna matuka tare da alkawarin kudi ga Yahuza, shi kuwa sai ya fara neman zarafin da zai mika Yesu a gare su. 12 A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti da kuma hadayar ragon Idin ketarewa, almajiransa suka ce masa “Ina zamu shirya liyafar domin idin ketarewa? 13 Ya aiki biyu daga cikin almajiransa da cewa “Ku shiga cikin birnin, zaku tarar da wani mutum dauke da tullun ruwa. 14 Duk gidan da ya shiga ku bishi, sai ku cewa mai gidan, malam yace “ina bukatar masauki domin hidimar idin ketarewa tare da almajiraina?”' 15 Zai kuwa nuna maku babban bene gyararre. Sai ku yi mana shiri a can.” 16 Da shigar almajiran cikin birnin, sai kome ya kasance yadda ya fada, su kuwa suka yi shirye shiryen idin ketarewar. 17 Da maraice ta yi, sai ya tare da sha biyun. 18 Yayin da suke zazzaune a teburin suna cin abincin, sai Yesu ya ce “Hakika ina gaya maku wani da ke ci tare da ni a nan zai bashe ni”. 19 Sai suka damu suka tambaye shi daya bayan daya suna cewa “Hakika bani bane ko?” 20 Yesu ya amsa masu da cewa “Daya daga cikin sha biyu ne, wanda ke sa hannu tare da ni yanzu cikin tasar”. 21 Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! “zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba”. 22 Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya dauki gurasa ya sa albarka, ya gutsuttsura ta, sai ya basu yana cewa “Wannan jikinana ne”. 23 Ya kuma dauki koko, yayi godiya, ya basu, su kuwa suka sha daga kokon. 24 Ya ce “Wannan jinina ne na alkawari da an zubar ga yawancin mutane”. 25 Hakika, bazan kara sha daga wannan ruwan inabi ba sai a ranar da zan sha sabo cikin mulkin Allah.” 26 Bayan sun raira wakar yabo ga Allah, sai suka tafi wurin dutsen zaitun. 27 Yesu ya ce masu dukkan ku zaku yi tuntube harma ku fadi saboda ni gama rubuce take cewa “Zan buge makiyayin, tumakin kuwa za su watse; 28 Amma bayan tashina, zai yi gaba in riga ku zuwa Galili. 29 Bitrus ya ce masa “ko dukkansu sun fadi, faufau banda ni”. 30 Yesu yace masa “Hakika ina gaya maka, cikin wannan dare kafin carar zakara ta biyu zaka yi musun sani na sau uku”. 31 Amma Bitrus ya sake cewa “Koda za'a kasheni tare da kai ba zan yi musun sanin ka ba”. Dukkan su kuwa suka yi wannan Alkawari. 32 Suka isa wani wuri da ake kira Getsamani, sai Yesu ya ce wa almajiransa “Ku dakata anan domin zan je inyi addu'a”. 33 Sai ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya. Ya fara jin wahala mutuka tare da damuwa kwarai. 34 Sai ya ce masu “Raina na shan wahala harma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a fadake”. 35 Da Yesu yayi gaba kadan, sai ya fadi kasa yayi addu'a yana cewa idan mai yiwuwa ne “A dauke masa wannan sa'a daga gare shi. 36 Ya ce “Ya Abba Uba, kome mai yuwane gare ka, ka dauke mini kokon wahalan nan, duk da haka ba nufina ba sai dai naka”. 37 Da komowarsa ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus, Siman barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a fadake ko da sa'a daya ba? 38 Ku zauna a fadake, kuyi addu'a kada ku fada cikin jaraba. Lalle ruhu na da niyya amma jiki raunana ne. 39 Sai ya sake komawa, yayi addu'a, yana maimaita kalmominsa na farko. 40 Har wa yau kuma ya sake dawowa, ya same su suna barci don barci ya cika masu idanu kwarai, sun kuwa kasa ce masa kome. 41 Ya sake komowa karo na uku yace masu “har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi”. 42 Ku tashi mutafi kun ga, ga mai bashe ni nan ya kusato.” 43 Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su. 44 Mai bashe shi din nan ya riga ya kulla da su cewa “Wanda zan yi wa sumba shine mutumin, ku kama shi ku tafi da shi a tsare. 45 Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce “Ya malam!”. Sai ya sumbace shi. 46 Su kuwa suka kama shi, suka tafi da shi. 47 Amma daya daga cikin na tsaye ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya yanke masa kunne. 48 Sai Yesu ya ce “kun fito kamar masu kama yan fashi da takkuba da kulake, domin ku kama ni? 49 Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada.” 50 Daga nan duk wadanda suke tare da Yesu suka yashe shi, suka tsere. 51 Wani saurayi, daga shi sai mayafi ya bi shi, suka kai masa cafka. 52 Shi kuwa ya bar masu mayafin ya gudu tsirara. 53 Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. a can suka tara dattawa duk da manyan firistoci da shugabanni da marubuta, suka taru a wurinsa. 54 Bitrus kuwa ya bi shi daga nesa har cikin gidan babban firist. Ya zauna tare da dogaran Haikalin, yana jin dumin wuta. 55 Sai, manyan firistoci da duk 'yan majalisa Yahudawa suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi. Amma basu samu ba. 56 Da yawa kuma suka yi masa shaidar Zur (Karya), amma bakin su bai zama daya ba. 57 Sai wadansu kuma suka taso suka yi masa shaidar zur (karya) suka ce. 58 “Mun ji ya ce, wai zai rushe haikalin nan da mutane suka gina, ya sake gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba”. 59 Duk da haka, sai shaidar tasu bata zo daya ba. 60 Sai babban firist ya mike a tsakanin su, ya tambayi Yesu yace “Ba ka da wata amsa game da shaidar da mutanen nan suke yi a kanka? 61 Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa “To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki? 62 Yesu ya ce “Nine. Za ku kuwa ga Dan Mutum zaune dama ga mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare”. 63 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa yace “Wacce shaida kuma zamu nema? 64 Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa. 65 Wadansu ma suka fara tottofa masa yau, suka daure masa idanu, suka bubbuge shi suna cewa “Yi annabci” Dogaran kuma suka yi ta marinsa. 66 Bitrus kuwa na kasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo. 67 Da ta ga Bitrus na jin dumi, ta yi masa kallon gaske ta ce “Kaima ai tare kake da banazaren nan Yesu”. 68 Amma ya musa ya ce “Ni ban ma san abinda kike fada ba balle in fahimta”. Sai ya fito zaure. Sai zakara yayi cara. 69 Sai baranyar ta ganshi, ta sake ce wa wadanda ke tsaitsaye a wurin, “Wannan ma daya daga cikinsu ne”. 70 Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus “Lalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai”. 71 Sai ya fara la'anta kansa yana ta rantsuwa yana ce wa “Ban ma san mutumin nan da kuke fada ba”. 72 Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku”. Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.