15
1 Da sassafe, sai manyan firistoci suka hadu da dattawa da manyan malamai, da majalisa suka daure Yesu, suka sa shi gaba suka mika shi ga Bilatus.
2 Bilatus ya tambaye shi, kaine sarkin Yahudawa? ya amsa ya ce “haka ka ce”
3 Sai manyan firistochi suka kawo zargi iri iri a kan Yesu.
4 Bilatus ya sake tambayarsa, ba ka da abin cewa? ka lura da yawan zargi da ake yi maka.
5 Amma Yesu baya sake yi masa magana ba. wannan ya ba shi mamaki.
6 A lokacin idi, Bilatus ya kan sakar masu da dan bursuna wanda jama'a suka bukaci a saka,
7 A cikin gidan yari, in da aka tsare wadansu yan tawaye, da masu kisan kai, akwai wani mai kisan kai, ana ce da shi Barrabbas.
8 Sai Jama'a suka zo wurin Bilatus ya yi masu kamar yadda ya saba yi.
9 Bilatus ya amsa masu ya ce, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?
10 Yayi wannan domin ya sani cewa Firistoci sun bada shi ne domin suna kishin sa,
11 Sai Firistochi suka zuga jama'a, sai suka yi kuwwa suna cewa, a sakar masu Barrabbas amaimakon Yesu.
12 Bilatus ya sake yi masu tambaya “Yaya zan yi da Sarkin Yahudawa?”
13 sai suka amsa da kuwwa” a “giciye shi!”
14 Bilatus ya ce masu menene laifinsa sai suka kara ihu, “a giciye shi.”
15 Bilatus don yana son ya farantawa jama'a zuciya sai ya sakar masu da Barrabbas sai ya yi wa Yesu bulala, sannan ya mika shi a giciye shi.
16 Sojoji suka kai shi cikin kagara, suka tara rundunan soja,
17 Suka sa masa tufafin shulaiya suka nada masa rawanin kaya,
18 Suna masa kirari na ba'a suna cewa, “A gaida sarkin Yahudawa!”
19 Sai suka buge shi a kai da kulki suka kuma tofa masa yau a fuska, suka kuma durkusa suna yi masa sujadar ba'a.
20 Bayan sun gama yi masa ba'a sai suka cire masa tufafin shunnaiya, sai suka maida masa tasa tufafinsa, sai suka fitar dashi don su giciye shi.
21 Suna cikin tafiya sai suka hadu da wani, mai suna Saminu Bakairawani (wato uban Alizanda da Rufus); suka tillasta shi ya dauki gijiyen Yesu.
22 Sojojin suka kawo Yesu wurin da ake kira Golgota (wato kokon kai)
23 Suka bashi ruwan inabi hade da mur, amma ya ki ya sha.
24 Sai suka giciye shi, suka kuma raba tufafinsa suka kuma jefa kuri'a domin kowanne soja ya sami rabonsa.
25 A sa'a ta uku aka giciye shi.
26 Sai aka rubuta alamar zargi da take cewa “Ga Sarkin Yahudawa”
27 Suka kuma giciye shi tare da wadansu yan fashi guda biyu.
28 Daya a hannun damansa daya a hannun hagunsa. Domin a cika abinda nassi ya fada.
29 suke wucewa suna zaginsa suna kada kai suna cewa, “Aha! kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku,
30 ka ceci kanka mana, ka sauka daga giciye!”
31 Haka ma manyan firistoci da malamai, suka yi masa ba'a suna cewa “Ya ceci wadansu amma bai iya ceci kansa ba”
32 Bari Almasihu Sarkin Yahudawa ya sauka daga giciye. Domin mu gaskata shi, sai wadanda aka giciye shi tare dasu, suma suka yi masa ba'a.
33 sa'a ta shida zuwa sa'a ta tara, duhu ya rufe ko'ina,
34 A sa'a ta tara, Yesu ya tada murya da karfi ya ce Eloi, Eloi lamathsabathani?” Ma'ana Ya Allahna Ya Allahna, me ya sa ka yashe ni?”
35 Wasu daga cikin na tsaye, da suka ji shi, sai suka ce, “Duba, yana kiran Iliya.”
36 Sai wani ya hanzarta, ya dauki soso ya tsoma a ruwan inabi mai tsami, ya soka agora ya mika masa don yasha. Mutumin yace bari mu gani ko Iliya zai zo ya saukar da shi.
37 Sai Yesu yayi kuka da babban murya da karfi sannan ya rasu.
38 Sai labulen haikalin ya rabu kashi biyu daga sama har kasa.
39 Sa'adda da jarumin sojan da ke tsaye yana fuskantar Yesu ya ga yadda ya mutum, Sai ya ce “hakika, wannan mutum Dan Allah ne.”
40 Akwai kuma mata wadanda ke dubawa daga nesa. Daga cikinsu akwai Maryamu Magadala, da Maryamu( Uwar Yakubu da Yusufu) da Salome.
41 Wadannan matan sune suka bishi sa'adda da yake Galilee suna yi masa hidima. Da wadansu mata da yawa suka zo Urushalima tare da shi.
42 Da maraice an shiga shirye shirye domin kashe gari asabbaci ce.
43 Sai Yusufu daga garin Arimatiya ya zo, mutumin kirki, mai girma kuma dan majalisar dattawa, mai sauraron mulkin Allah, da gaba gadi ya tafi wurin Bilatus ya bukaci a bashi jikin Yesu.
44 Bilatus ya yi mamakin mutuwar Yesu cikin lokaci kadan, sai ya kira jarumin ya tabbattar koYesu ya mutu.
45 Bayan ya tabbattar daga wurin jarumin soja cewa Yesu ya mutu, sai ya bada jikin ga Yusufu.
46 Yusufu ya sayo likafani. ya saukar da shi daga giciye, ya kawo likafanin nan ya lulube jikin Yesu dashi. Ya kai shi kabarin da aka sassaka da dutse, wadda ya shirya shi domin kansa. Ya kawo dutse ya rufe bakin kabarin da shi.
47 Maryamu Magadaliya da Maryamu Uwar Yusufu sun ga wurin da aka yi jana'izar Yesu.